Shugaban kwamitin shirin ciyar da daliban makaranta Frimare na kasa, ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su

Shugaban kwamitin shirin ciyar da daliban makaranta Frimare na kasa, ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su

- Bala Usman ya garagadi malaman makarantar frimare akan cinye wa dalibai abincin

- Za a gurfanar da duk wani malamin da aka kama da laifin cin abicin dalibai inji Mallam Usman

Malam Bala Usman, shugban kwamitin shirin ciyar da daliban makarantar Frimare da gwamnatin tarayya ta kaddamar (HGSPF) ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su.

Usman Bala, yayi wannan gargadi ne a wata hira da yayi manema labaru a ranar Talata.

Shugaban kwamitin shirin ciyar da daliban makaranta Frimare na kasa, ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su
Shugaban kwamitin shirin ciyar da daliban makaranta Frimare na kasa, ya gargadi malamai akan cinye wa dalibai abincin su

Legit.ng ta samu rahoton cewa, masu dafawa dalibai abincin sun yi korafin cewa, mallaman makaranta suna raba abincin dalibai a tsakanin su.

KU KARANTA : Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari

Mallam Usman, ya ce za su dauki tsatsauran mataki akan duk mallamin da aka kama da laifin cin abincin dalibai.

Usman ya kara da cewa za su ja hankalin masu dafawa dalibai abincin akan bai wa dalibai kadai abinci, sannan idan suka yi wani abu sabanin haka, za a hukunta su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel