Bayan shekaru 22, za a kafa Jami'ar Jiha ta farko a Zamfara

Bayan shekaru 22, za a kafa Jami'ar Jiha ta farko a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari ya bayyana cewa, jihar sa ta shirya tsaf domin kafa sabuwar jami'a ta farko bayan shekaru 22 da kafuwar jihar.

A ranar Litinin din da ta gabata gwamnan ya bayyana hakan a birnin Abuja, bayan karbar wasikar aminci ta hukumar jami'o'i wato NUC na kafa jami'ar a garin Talata Mafara.

A yayin bayar da wannan sanarwa Yari ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 3 na fara gudanar da aikace-aikace a jami'ar.

Abdulaziz Abubakar Yari
Abdulaziz Abubakar Yari

Gwamnan ya ci gaba da cewa, za ayi amfani da Naira biliyan daya wajen horas da ma'aikata, naira biliyan daya ta sayen kayan aiki yayin da kuma aka ware naira biliyan daya domin fara gine-gine a jami'ar.

KARANTA KUMA: Illa daya da Shinkafa ta kunsa ga lafiyar dan Adam

Yari ya kara da cewa, bayan kafuwar jihar shekaru 22 da suka gabata, jihar Zamfara ta kasance jiha daya da ba ta da jami'ar jiha a duk fadin Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daya daga cikin manufofin kafa wannan jami'a shine samar da kwararrrun kiwon lafiya wanda a halin yanzu sun yi karanci a ma'aikatun jihar.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau ne matasa zasu dunguma zuwa fadar shugaban kasa ta Villa domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng