Dalilin da yasa na bayyana albashin sanatoci – Shehu Sani

Dalilin da yasa na bayyana albashin sanatoci – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawan tarayya ya bayyanawa duniya cewa shi da abokan aikinsa kan amshi N13.5 million a wata domin ayyukan jin dadinsu sabanin albashin da suke samu.

A wata hira da yayi da BBC, Shehu Sani ya bayyana dalilin da ya sa yayi hakan.

Yace: “Na yanke shawaran bayyanawa ne saboda kare mutunci,

Ya ce ana gudanar da majalisan dokokin tarayya cikin rashin gaskiya kan yadda aka kasha kudade.

Dalilin da yasa na bayyana albashin sanatoci – Shehu Sani
Dalilin da yasa na bayyana albashin sanatoci – Shehu Sani

Yana son a daina biyan Sanatoci kudin Haram saboda maras aikinyi su daina takara zaben majalisa kowani shekaran zabe.

“Majalisan dokokin tarayya na daga cikin ma’aikatun gwamnati da rashin gaskiya yafi yawa. Na duba al’amarin sai nay a kamata in bayyanawa duniya kowa ya gani.”

“Idan aka daina biyan wadannan kudade, wadanda basu da manufa na kwarai zasu daina zuwa majalisan,”

Sanata Shehu Sani ya yi bayani a wata hira da jaridar The News cewa suna karban N13.5 million a wata sabanin N750, 000 kudin albashi sannan wasu alawus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng