Maryam Sanda ta mayar da martani a kan yamadidi da batun yiwa 'yar ta biki
- Maryam Sanda ta musanta batun yiwa diyar ta bikin ranar zagayowar ranar haihuwa kwana daya kacal bayan bayar da belinta
- Dangian Maryam Sanda sun ce an dauki yarinyar hoto ne kawai amma babu wani biki da aka yi
- Dangin sun ce hoton da aka yi ya fi wata daya da dauka
Maryam Sanda, matar dake fuskantar tuhumar kotu bisa zarginta da kisan mijinta, Bilyamin Muhammed, dan tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Halliru Bello.
A satin da ya gabata ne kotu ta bayar da belin Maryam Sanda kuma kwana daya kacal sai ga rahotanni sun bayyana cewar tayi bikin ranar zagayowar ranar haihuwa diyar ta.
A wani jawabi da dangin Sanda su ka fitar, sun musanta batun dake yawo a gari na cewar tayi biki kwana daya kacal bayan bayar belinta.
DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Sai matafiya sun biya kudi kafin su yi amfani da bandaki a filin jirage na Kano
Dangin nata sun ce hoton da ake yamadidi da shi, an dauke shi ne fiye da wata guda kuma sun aike da hoton ne ga wasu 'yan uwa na kusa amma sai gashi wasu manema labarai sun sayi hotunan suna ta yamadidi da batun a kafafen watsa labarai da dandalin sada zumunta.
Mai shari'a Yusif Halilu ya bayar da belin Maryam Sanda ne ranar Laraba, 7 ga watan Maris, bisa dalilan rashin koshin lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng