Buhari a Benuwe : Kabilar Tiv suna fushi da kai - Akume ya fada wa shugaban Kasa
- Shugaba Buhari ya ziyarci jihar Benuwe a ranar Litinin
- Goerge Akume ya sanar da Buhari cewa mutanen kabilar Tiv sun fushi da shi
Tsohon gwamnan jihar Benuwe kuma Sanata a majalissar Dattawa, Mista George Akume, ya sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, cewa mutanen 'yan Kabilar Tiv suna fushi da shi, saboda nuna halin ko’in kula da yayi akan kashe-kashen da aka yi jihar.
Akume ya ce ida aka tuna baya, mutanen jihar Benuwe suna cikin wadanda suka ba shugaba Buhari, kur’iu da yawa a zaben 2015 duk da kasancewar, Sanata David Mark, tsohon shugaban majalissar dattawan Najeriya, dan jihar ne.
Akume yayi kira da shugaban kasa ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar Benuwe.
KU KARANTA : Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi
"Babu wani aiki da gwamnatin tarayya ta yiwa mutanen jihar Benuwe, Mai girma shugaban kasa, ya sani cewa mutanen jihar Benuwe suna fushi da shi saboda nuna rashin damuwa da yayi akan kashe ‘yan kabilar Tiv da Fulani makiyaya suke yi a jihar," Inji Akume .
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng