Shugaba Buhari ya gana da manoma, Miyetti Allah da dattawan Benue
Shugaba Muhammadu Buhari yana ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar Benue wanda ya kunshi manoma, kungiyar Miyetti Allah da dattawan Benue kan kasha-kashen da ke faruwa a jihar.
Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Benue. Shugaban kasan ya dira filin jirgin saman Makurdi misalign karfe 10:43 na safe.
Daga cikin wadanda ke halartan taron sune wakilan Miyyeti Allah, Manoma, masu gadin dabbobi, Mzough U-Tiv, da sauran su.
Yayin ganawar da aka yi a gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi, wakilan kungiyoyin sunyi bayani filla-filla kan kasha-kashen da ke faruwa.
KU KARANTA: Duk wanda aka kama ya mallaki budurwar danko zai ta fi kurkuku - Zambia
Kungiyar Miyetti Allah ta musanta hannu cikin kasha-kashen da ke faruwa. Su kuma manoma sun bukaci shugaba Buhari ya taimaka wajen kawo karshen wannan abu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng