Jami’an Sojoji sun damke wani mai garkuwa da mutane

Jami’an Sojoji sun damke wani mai garkuwa da mutane

- Jami’an tsaro sun kai hari a wani daji a cikin Garin Okene a jiya

- An yi nasarar damke wani hatsabibi da ya ke garkuwa da mutane

- Yanzu haka dai ana kokarin cigaba da gano masu ta’asa a Yankin

Rundunar Sojojin Najeriya sun damke wani gagararren mai laifi wanda ya addabi Jama’a a Jihar Kogi bayan wani hari da Sojojin su ka kai a Garuruwan Irovovochinomi da Egee da ke cikin Jihar. Har yanzu haka dai ana kan aikin.

Jami’an Sojoji sun damke wani mai garkuwa da mutane
Sojojin Najeriya sun shiga daji sun kamo mai garkuwa da mutane

An damke wannan gawurtaccen mai garkuwa da mutane ne a cikin Karamar Hukumar Okene. Rundunar Sojin kasar sun yi ram da Mohammed Bashir wanda yana cikin wadanda su ka kashe wani kurtun Soja kwanakin baya.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun tsawatar kan kashe-kashen da ake yi

An samu wannan mai gaurkuwa da mutane dauke da makamai na bindigar AK 47 da harsashi rututu. Wata runduna ta musamman ce dai aka tura domin kamo wannan fitinannen mai laifi a jiya Ranar Lahadi kamar yadda mu ka ji.

Darektan yada labarai na gidan Sojan kasar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana wannan a shafukan sadarwa na Sojojin kasar. Sojojin na neman duk wani karin bayani da zai taimaka wajen ganin kawo karshen miyagu a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng