'Yan bindiga cikin kakin soji sun kai hari a Katsina, mutane uku sun mutu

'Yan bindiga cikin kakin soji sun kai hari a Katsina, mutane uku sun mutu

- Wani hari da ake zargin 'yan fashi da kaiwa a kauyen Tandama dake karamar hukumar Danja ya yi sanadiyar kashe wani mazaunin kauyen

- An kashe biyu daga cikin 'yan bindigar dake sanye da kakin soji a musayar wuta da jami'an 'yan sanda

- Hukumar 'yan sanda ta ce ta tura rundunar jami'anta masu yaki da fashi da makami domin cafko ragowar 'yan bindigar

Mutane uku ne aka tabbatar da sun rasa ransu yayin da wasu 'yan bindiga su ka kai hari kauyen Tandama dake karamar hukumar Danja a jihar Katsina.

Wani shaidar gani da ido da aka kashe dan uwansa ya ce 'yan bindigar, cikin kakin soji, sun dira a kauyen da misalin karfe 1:15 na safiyar ranar Asabar dauke da bindigu kirar AK 47. 'Yan bindigar sun kai farmaki gidajen Alhaji Safiyanu da Abdullahi Tandama.

'Yan bindiga cikin kakin soji sun kai hari a Katsina, mutane uku sun mutu
Gwamna Masari

Saidai, tirjewar da mutanen kauyen su ka yi tare da tunkarar 'yan bindigar ya yi sanadiyar mutuwar biyu daga cikin 'yan fashin yayin da su ka kashe mutum daya daga mutanen garin.

"Dan uwana na kawance a waje sai su ka ji karar harbin kuma su ka tashi tare da tunkarar 'yan fashi domin hana su aikata abinda su ke da niyya. Saboda mutanen garin na da yawa, sun yi nasarar fin karfin 'yan bindigar tare da hallaka biyu daga cikinsu yayin da su kuma su ka kashe dan uwana sannan su ka gudu bayan jin isowar 'yan sanda."

DUBA WANNAN: Harin Rann: Hukuma ta fitar da adadin soji, 'yan sanda da su ka mutu

Saidai hukumar 'yan sanda a jihar Katsina ta bayyana cewar 'yan bindigar biyu sun mutu ne yayin musayar wuta da jami'an ta.

Kazalika hukumar ta sanar da baza jami'anta masu yaki da fashi da makami domin cafko ragowar 'yan bindigar da su ka gudu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel