Riginginmu shida a APC da zasu yiwa kwamitin Tinubu wahalar sulhuntawa

Riginginmu shida a APC da zasu yiwa kwamitin Tinubu wahalar sulhuntawa

A farkon watan Fabrairun wannan shekarar ne jam'iiyar APC ta kafa wata kwamitin sulhunta mambobin jam'iyyar karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu ya gana da shugaba Buhari kafin daga bisani ya ziyarci Sakatariyar jam'iyyar a Abuja inda ya gana da wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar, daga bisani kuma ya gana da wasu kusoshi a jam'iyyar da suka hada da Bukola Saraki, Rabiu Musa Kwankwaso, Aminu Tambuwal da sauran su.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, kwamitin na Tinubu ta fara gudanar da ayyukan ta gadan-gadan sai matsalar da ta faru tsakanin Tinubu da Ciyaman din kwamitin gudanarwa na jam'iyyar, Mr. John Odigie-Oyegun ya saka kwamitin ta ja baya kadan.

A halin yanzu, akwai wasu rigingimu guda shida da ake gannin zasu yiwa kwamitin na Tinubu wahalar warware wa.

1) Kano

A jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba su ga maciji, duk da yunkurin sulhunta su a baya da akayi, yan siyasa biyu sun bayyana cewa basu da sha'awar aiki tare a nan gaba.

A makon da wuce, Gwamna Ganduje ya aurar da diyar sa ga dan Gwamna Ajimobi na jihar Oyo amma Kwankwaso bai hallarci daurin auren ba. Daga baya ma har sukar auren yayi inda ya ce "ya yi mamakin yadda mutane suka bata lokacin kan auran zaurawa".

KU KARANTA: Wani masanin al'ummuran matasa ya sake janyo hankalin Buhari kan batun Peace Corps

2) Kaduna

Rikicin na Jihar Kaduna yana daga cikin ababen da wasu ke ganin ya tabarbare da yawa, da farko dai jam'iyyar ta rabu kashi uku a jihar. Kashi na farko mai kiran kanta 'Restoration APC' karkashin jagorancin Tijjani Ramalan, kashi na biyu 'APC Akida' karkashin jagorancin Sanata Shehu Sani sai kuma na uku mai shine 'APC na gidan gwamnati' wanda suke tare da Gwamna El-Rufai.

Sashin da tare da Tijjani Ramalan ta dakatar da El-Rufai inda shi kuma ya yi amfani da Hukumar kula da gine-gine na jihar wajen rushe Sakatariyar yan aware din. A takaice dai zaman doya da manja akeyi.

3) Zamfara

A Zamfara kuma Gwamna Abdulaziz Yari ne ke gwabzawa da Sanata Kabiru Marafa. Rikcin nasu ya samu asalin ne a shekarar bara lokacin da aka nada Ahmed Mahmoud a matsayin kwamishinan zabe na jihar amma Yari yaki amincewa bisa dalilin cewa Mahmoud ba dan jihar Zamfara bane.

Daga baya ya rubuta wasika zuwa ga Majalisar Dattawa inda ya bukaci a sauke shi daga matsayin kuma tun lokacin gaba da kullu tsakanin kusoshin APC a jihar.

4) Sokoto

A jihar Sokoto kuma wani jigo a jam'iyyar, Muhammad Bashar ne ke zargin Gwamna Aminu Tambuwal da yin watsi da mambobin jam;iyyar yan asalin tsohuwar jam'iyyar CPC.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kafa jam'iyyar ta CPC amma daga baya sukayi maja don kafa APC.

5) Kogi

A jihar Kogi dama an dade ana musanyar munana kalamai tsakanin Gwamna Yahaya Bello da Sanata Dino Melaye. A yanzu kuma wata sabuwar rikici ta barke tsakanin wadanda ke biyaya da gwamna da kuma sauran mambobin kwamitin dattawa na jam'iyyar.

Rigimar ta barke ne bayan sashin da ke biyaya ga Gwamna Yahaya sun fitar da sanarwan korar Ciyaman din jam'iyyar Hadi Ametuo.

Sai dai daga baya, Sakatariyar kasa na jam'iyyar tace babu wanda ya ke da ikon korar ciyaman din ba tare da tuntubar Kwamitin zartarwa na kasa ba.

6) Adamawa

Wata rikicin da ke bukatar kwamitin na Tinubu ta mayar da hankali kan ta shine rihimar da ke tsakanin tsohon Gwamna Murtala Nyako da kuma gwamna mai ci yanzu, Mohammed Jibrilla.

Magoya bayan yan siyasar biyu sun ware kansu kuma ba su ga maciji.

Sauran matsalolin da kwamitin na Tinubu ya kamata ta duba sun hada da rigimar Gwamna Kashim Shettima da Sanata Abubakar Kyari, Sanata David Umaru, Sanata Aliyu Abdullahi da Gwamna Sani Bello, Magnus Ibe da Rotimi Amaechi da kuma rikicin da ke tsakanin John Oyegun da Timi Frank.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel