Kotu ta bayar da umurnin a damko wani Sanatan jam'iyyar APC

Kotu ta bayar da umurnin a damko wani Sanatan jam'iyyar APC

- Wata kotu da ke zama a babban birnin Tarayya Abuja ta bayar da umurnin cewa a taso keyar Sanata mai wakiltan yankin kudancin Anambra

- Kotun ta bayar da umurnin ne bayan wata kungiyar mai zaman kanta ta shigar da kara a kan Sanata Andy Uba

- Kungiyar tana fatar kotu zata fara gudanar da bincike kan Sanatan saboda laifin amfani da shedar jarabawar karatu (WAEC) na bogi da tace yana amfani dashi

Wata kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta bayar da umurnin damko Sanata mai wakiltan yankin kudancin Anambra, Andy Uba sakamakon karar da wata kungiyar yaki da cin hanci mai suna 'Anti Corruption Integrity Forum' (ACIF) ta shigar.

Kotun ta amince da bukatar kungiyar na tursasa babban Alkalin Alkalai na kasa da Sifeta Janar na Hukumar Yan sanda su bayar da umurcin kama Uba bisa zargin sa da amfani da sakamakon karatun kamalla sakandare (WAEC) na bogi.

Kotu ta bayar da umurnin a damko wani Sanatan jam'iyyar APC
Kotu ta bayar da umurnin a damko wani Sanatan jam'iyyar APC

A yayin da take yanke hukunci kan karar da kungiyar ta shigar, Mai shariah Binta Nyako ta amince da bukatar na kungiyar mai zaman kanta wanda aka shigar ta hannun lauyan kungiyar, Amobi Nzelu.

KU KARANTA: Maryam Sanda ta shirya wa diyar ta buki kwana daya bayan bayar da belin ta, ku kalli hotuna

A wata takardan shaida da wani ikechukwu Godswill ya rubuto, ya bayyana cewa a ranar 24 ga watan Afrilun 2017, wata ofishin lauyoyin mai suna Anhony Agbolahor ta rubuta wasika zuwa ga mataimakin Sifeta Janar na yan sanda a madadin Victor Uwajeh bisa zargin Andy Ubah da amfani da sakamakon jarabawar WAEC na bogi.

Hakan yasa ofishin mataimakin Sifeta Janar na Yan sanda ta rubuta wasika zuwa ofishin WAEC don tantance sakamakon jarabawar inda daga baya WAEC ta tabbatar da cewa sakamakon da Uba ya ke amfani dashi na bogi ne.

Hakan yasa aka gayyaci Uba zuwa ofishin yan sanda don ya amsa tambayoyi kan lamarin a ranar 31 ga watan Augusta na 2017 amma hakan bai yiwu ba saboda wasu dalilai da suka taso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164