Shugaba Buhari zai kaddamar da katafaren kamfanin sarrafa suga a Neja
- Kamfanin Flour Mills Plc ta bayyana cewa nan da kankanin lokaci za ta kammala shirye-shiryen kaddamar ta masana'antar sarrafa suga a jihar Neja
- Aikin gina masana'antar zai lashe kudi naira biliyan 50 kuma an sa ran masana'antar zata rika samar da metric ton 100,000 a duk shekera
- Shugaba kasa Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da masana'antar suga idan an kammala
Kamfanin Sarrafa flawa na 'Flour Mills Nigeria Plc' ta bayyana cewa tana kusa kamalla shirye-shiryen kadammar da sashin sarrafa suga na kamfanin mai suna 'Sunti Golden Estate' da za'a bude a garin Mokwa na jihar Neja.
Masana'antar sugan da zai lashe maukuden kudi har naira biliyan 50 zai rika samar da sukari da adadin sa ya kai metric ton 100,000 a duk shekara.
KU KARANTA: Aisha Buhari ta aike da muhummiyar sako ga Boko Haram cikin faifan bidiyo
Sanarwan da ta fito daga jami'an hulda da al'umma na kamfanin, Tola Samuel, ya ce ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da masana'antar a ranar Alhamis, 15 ga watan Maris kamar yadda NAN ta ruwaito.
Sanarwan kuma ta ce gona sukari mai fadin hecta 17,000 da za rika samar wa masana'antar da rake zai samar ga ayyukan yi ga manoma 10,000 a duk shekara kuma kimamanin mutane 50,000 za su amfana ciki har da kananan manoma 3,000.
Ana sa ran masana'antar za ta rage adadin sugar da Najeriya ke siyowa daga kasashen waje kuma ta habbata tattalin arziki da rage talauci ta hanyar samar wa yan Najeriya ayyukan yi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng