‘Yan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane biyu a jihar Sakkwato

‘Yan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane biyu a jihar Sakkwato

- Hukumar Yan sanda ta cafke wasu masu garkuwa da mutane biyu a jihar Sakkawato

- Mutanen biyu sun kira wata mata, Fatima Shehu ne a waya kuma suka bukaci ta basu N2m ko kuma su sace mata yaran ta biyu

- Fatima Shehu ta kai kara ofishin yan sanda kuma anyi nasarar kama mutanen biyu kuma sun amsa laifin na su

Hukumar ‘Yan Sanda ta jihar Sakkwato ta kama wasu mutane biyu bisa zargin satar mutane, Awaisu Isah mai shekaru 20, da kuma kabiru Lawali mai shekaru 25, bisa zargin kitsa makirci, tsoratarwa da kuma kwace.

A yayin gabatar da wadanda ake zargi ga manema labarai, Kakakin Hukumar Yan sanda, ASP Cordelia Nwawe ta shaida wa jaridar Northern City News cewa an kama mutanen biyu ne bayan wata mai suna Fatima Shehu ta shigar da kara.

‘Yan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane biyu a jihar Sakkwato
‘Yan Sanda sun kama masu garkuwa da mutane biyu a jihar Sakkwato

Fatima ta fadawa hukumar yan sanda cewa mutanen sun kira ta a waya ne sunyi mata barazanar sace mata yara biyu idan bata basu kudi N2m ba.

KU KARANTA: Kungiyoyin ma'aikata suna barazana ga cigaban Najeriya - El-Rufai

Bayan sun shiga hannu, masu laifin sun amsa cewa gaskiya ne sun kira Hajiya Fatima a waya sun yi mata barazana a kan kudi.

An kara tasa keyar wani mai suna Naziru Muhammad, mai aikin duba kaya a filin Jirgi na Sultan Abubakar III, wanda ya amsa laifin satar wani katon guda daya, mai dauke da nau’o’I 120 na waya mai kirar Tecno T528 wanda aka kiyasta kudinsu ya kai darajar N822,000

Wayoyin dai mallakar Earnest Onuorah, Dan Kasuwa a Hajiya Halima Albarka GSM market, garin Sakkwato.

Bayan zurfafa bincike, an sake kamo Mubarak Mustafa, Abubakar Muhammad, Sulaiman Ahmed da Mubarak Musa, wanda aka samu da wayoyin hannu guda 30, wanda suke ikirarin sun sayi kowace akan N4,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164