To fa: Trump zai gana da shugaban Koriya ta Arewa a watan Mayu

To fa: Trump zai gana da shugaban Koriya ta Arewa a watan Mayu

- Trump ya amince da gayyatar da shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa yayi masa

- Ya amince zasu gana a cikin watan Mayu na wannan shekarar

- Shugaba Kim Jong Un ya amince da takunkumin da kasar ta Amurka ta sanya masa na gwajin makamai masu linzami

To fa: Trump zai gana da shugaban Koriya ta Arewa a watan Mayu
To fa: Trump zai gana da shugaban Koriya ta Arewa a watan Mayu

Fadar shugaban kasa ta White House ta ce shugaba Donald Trump ya yarda da gayyatar tattaunawar sulhu da shugaba Kim Jong Un na koriya ta Arewa yayi masa, Sai dai duk da hakan za a cigaba da sanya wa kasar takunkumin.

DUBA WANNAN: Ziyarar Shugaba Buhari jihar Rivers baza ta saka matacciyar jam'iyyar APC ta tashi jihar ba - Wike

Shugaba Kim Jong Un ya yi bayanin ganawa da shugaba Donald Trump din, ta hanyar mai bawa shugaban kasar Koriya ta Kudu shawara akan harkar tsaro, Chung Eui-yong, wanda ya kai ziyara kasar Koriya ta Arewa a makonnin baya.

Chung ya bayyana aniyar shugaba Kim Jong Un, a gaban fadar White House a jiya Alhamis da daddare, inda hakan ya zama abin mamaki a duniya baki daya.

Ba a jima da bayyana aniyar shugaba Kim din ba, sai shugaba Donald Trump ya bayyana sakon a shafin sa na twitter inda ya ke cewa:

"Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa yayi bayanin kawar da makaman nukiliya na kare dangi tare da wakilin Koriya ta Kudu. Sannan kuma Koriya ta Arewa ta amince da dokar gwada makamai masu linzami a wannan lokaci. Saboda haka ina ganin kamar an fara samun gagarumin cigaba."

Wata mai magana da yawun fadar White House Sarah Sander Hukabee ta bayyana a cikin shafin ta na twitter cewa shugaba Donald Trump ya amince zasu gana da shugaban kasar Koriya ta Arewa.

Chung ya ce shugaba Donald Trump ya bayyana masa cewa zasu gana da shugaba Kim Jong Un daga nan zuwa watan Mayu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: