Wasu matasa sun yi ma wani Mahaukaci rubdugu a unguwar Fagge har sai da yace ga garinku
Rundunar Yansandan jihar Kano ta cika hannu a wasu mutane guda uku da ake zargi da hannu cikin kisan wani mutumi mai tabin hankali Aminu Ishaq a unguwar Fagge ta jihar Kano, inji rahoton Dail Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Aminu ya cika ne a Asibitin Murtala na jihar a sakamakon rauni da ya samu biyo bayan lakada masa duka da mutanen suka yi a ranar Juma’ar da ta gabata, kan zarginsa da afkawa cikin gidansu ba tare da izini ba.
KU KARANTA:
Rahotanni sun tabbatar da an karya ma Aminu kafa da hannu a yayin da ake jibgarsa, inda Kaakakin rundunar Yansandan jihar Magaji Musa Majia ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka sun kama mutune uku dake da hannu cikin rubdugun.
Majia yace Aminu ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya afka gidan wani mutumi mai suna Sanda Maibarewa a unguwar Fagge: “Zuwa yanzu mun kama mutane uku, kuma muna cigaba da farautar sauran don jin bahasin su, daga bisani kuma mu garzaya da su gaban Kotu. ”
Majia yace guda biyu daga cikinsu sun hada da Sani Shehu Yaro da Usman Shehu Yaro, mazauna gidan Sanda Maibarewa.
A wani sauyi mai cike da alamar tambaya, majiyar ta ruwaito wata mata, Ruqayyah Abdulrahman ta zargi Yansanda da kashe Aminu mahaukaci. Ruqayyah wanda ke daure a ofishin Yansanda dake Fagge a daren da aka kashe Aminu, ta sanar da iyalan Aminu cewa Yansanda ne suka hallaka musu dan uwa.
Sai dai da maganar ta fito, sai aka hangi Ruqayyah tana kuka a farfajiyar Caji ofis, tana cewa ta ga Aminu ya je ofishin Yansandan a daren da za’a kashe shi tsirara, inda Yansanda suka kora shi gida. “Da naji an kashe shi ne sai na yi zaton Yansanda ne suka kashe shi a haka, har na sanar da yan uwansa.” Ini ta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng