Kungiyar Malamai na kasa ta koka kan karancin malamai a Jihar Bauchi

Kungiyar Malamai na kasa ta koka kan karancin malamai a Jihar Bauchi

- Kungiyar malamai na kasa NUT reshen jihar Bauchi ta bayyana cewa adadin malaman da ke jihar sunyi karanci

- Kungiyar tayi kira da gwamnati tayi gagawan daukan kwararun malamai da za su koyar a makarantun birane da kauyuka a jihar

- Kungiyar kuma ta shawarci gwamnati ta tabbatar cewa makarantun kauyuka sun sami malamai kamar yadda takwarorin su na birane ke samu

Kungiyar Malaman makarantu na kasa (NUT), reshen jihar Bauchi ta ce adadin malamai frimare 26,000 da ake da su a jihar sunyi kadan idan akayi la'akari da yawan daliban da ke jihar.

Shugaban kungiyar na jihar, Danjuma Sale ne ya furta hakan a ranar Alhamis yayin da yake hira da jami'an kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) a garin Bauchi.

Kungiyar Malamai na kasa ta koka kan karancin malamai a Jihar Bauchi
Kungiyar Malamai na kasa ta koka kan karancin malamai a Jihar Bauchi

KU KARANTA: EFCC ta sake gurfanar da tsohon sakataren INEC bisa laifin karbar cin hanci daga Diezani

"Idan ka duba adadin malamai da muke da shi a jihar, guda 26,000 da muke da su sunyi kadan.

"Adadin malaman ba zai isa su koyar a duk makarantun jihar ba.

"A ka'ida, kowace makaranta tana bukatar malamai 15 - 30 musamman makarantun da ke da cikaken ajujuwa," inji shi.

Shugaban na NUT ya yi kira da gwamnatin Jihar ta hanzarta wajen magance matsalar karancin malaman da jihar ke fama da shi a hanyar dauka kwararun malamai da za su koyar a makarantun birane da karkara.

Sale ya jadada mahimmancin raba malaman ga makarantun da zuka dace ba wai na birane kawai ba.

"Galibin malaman suna makarantun birane ne da kuma hedkwatan, hakan ya sa makarantun karkara ba su samun malamai.

"Ya dace gwamnati ta dauki matakin ganin cewa dukkan makarantun sun sami malamai," inji shi.

Sale kuma ya yi kira ga malaman su zama masu kwazo wajen gudanar da aikin su a matsayin malamai da kuma iyayen yara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel