Rai fakwai mutu fakwai: Yadda wata Mata ta yi ma mijinta jinni da majina da taɓarya
Wata mata mai shekaru 28, Rita Ogubuenyi ta bazar da mijinta da tabarya biyo bayan wata karamar sa’insa da ta kaure a tsakaninsu, wanda yayi sanadiyyar zubewarsa rai fakwai mutu fakwai.
A ranar Laraba 7 ga watan Feburairu ne dai aka gurfanar da wannan mata a gaban Kotun majistri dake Ikeja na jihar Legas, inda ake tuhumarta da aikata laifuka guda biyu da suka hada da cin zarafi da tayar da zauni tsaye.
KU KARANTA: Hanyoyi 5 da za’a iya bi don kubuta daga kamuwa daga cutar zazzabin Lassa
Daily Trust ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar 10 ga watan Disambar da ta gabata a gidan ma’aurata,kamar yadda dansanda mai karaSajan Christopher John ya bayyana ma alkalin Kotun.
“Wanda ake tuhuma ta bazar da mijin nata ne da tabarya, bayan ya umarceta da kada ta fita tare da kawayenta, ta yi zamanta a gida tunda mutuncin ya mace gidan mijinta.” Inji Sajan John.
A cewar Dansandan, laifin ya ci karo da sashi na 172 da 166 na kundin hukunta manyan laifuka, inji rahoton majiyar Legit.ng, sai dai uwargida Rita ta tsaya kai da fata tana musanta tuhume tuhumen.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkali M.I Dan-Oni ta bada belin hukuncin Uwargida Rita akan kudi N100,000, tare da mutum guda da zai tsaya mata, kuma ta dage sauraron karar zuwa 27 ga watan Maris.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng