'Ina shigar manyan sojoji ne saboda anqi biya na kudin pansho' wani kurtu
- An kama sojan gona yana shigar manyan sojoji don damfara
- Yace yayi jiran duniya an qi biyansa fansho da garatuti
- Wasu manyan ne dai ke adana kudin kanana a banki don kudin ruwa ya hauhawa
Wani tsohon Soja mai suna Ali Audu, ya bayyana yanda yak e amfani da kayan na Soja har yanzu saboda hukumar ta Sojan Najeria basu biyashi kudin sallamar aikin ba. Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ahmed Iliyasu na helikwatar ‘Yan Sanda ta Eleweran Abeokuta, jihar Ogun yayi nasarar kama Audu, tare da wani Dan Sandan karya mai suna Ibrahim Ahmed.
Shugaban Hukumar ta ‘Yan Sanda, ya ce masu laifin sun kasance cikin mutane 24 da ake zargi da aikata laifuffukan su Fashi da Makami, Kisan Kai, Sata, da dai sauran su.
DUBA WANNAN: Ajinomoto na kawo cutuka - Bincike
Wanda ake zargin y ace ya aje aiki Watanni Biyar da suka wuce, ya kuma kara da cewa a duk shekaru 35 da yayi ya na aiki Albashin nashi bai wuce N84,000, wanda bai iya adanawa ba saboda hidimar yara.
Ba su biya ni kudin sallama ba da pansho na saboda haka nake amfani da wannan hanya don samun abun kula da iyali na. Ina amfani da kayan nawa ne saboda har yanzu suna hannu na dan a ka’idar aikin Soja har sai an sallame ka kayan na ka suna hannun ka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng