Za'a kammala tashan jirgin ruwa na kan tudu na Funtua a watan Mayu
- Cikin kwanakin nan za'a kamalla tashan jirgin ruwa na kan tudu na Funtua
- Hakan ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin Equatorial Marine Oil and Gas da aka bawa kwangilar aikin
- Aikin tashar jirgin ruwan na Funtua yana daya daga cikin ayyukan da Majalisar Zartarwa ta amince a fara tun shekarar 2006
Shugaban Kamfanin Equitorial Oil and Gas Ltd, Alhaji Umaru Mutallab, ya bayyana cewa, a cikin watan Mayu na shekarar nan ne ake sa rai za’a kammala tashan jirgin ruwa na kan tudu (Inland Container Depot) da ake gina wa a Funtua.
Dangane da wani jawabi, Alhaji Mutallab ya bayyana a wurin ziyara da suka kai na duba aiki tare da Sakataren Harkoki na Najeriya Shippers Counsil (NSC), Mr. Hasaan Bello. Ya ce Kamfanin wanda girmansa zai iya daukar Kwantena 10,000 tashin farko wanda zuwa gaba za’a iya kara fadada shi.
KU KARANTA: Yawan al'umma ne babban abin da muke alfahari da shi a Kano - Ganduje
"Kamfanin na Funtua Inland Dry Port wanda shine mafi girma a kasar nan zai kasance wuri na karshe da da za’a ringa sauke kaya, don haka zai bada damar da za’a fitar da kayan gona zuwa Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Da kuma kasashe masu tasowa kamar su Nijar, da Chadi zuwa wasu kasashe na Duniya," in ji Mutallab.
Za’a iya tunawa da cewa aikin na tashan jirgin ruwa na kan tudu na Funtua na daya daga cikin tashoshin kasa da Majalissaar Zartarwa ta Tarayya ta bayar da izini a fara tun Shekara ta 2006, an kuma kaddamar da ita ga Equatorial Marine Oil and Gas (EMOG), ya kuma dogara ne da tsarin da Gwamnatin Tarayya tayi wanda aka wakiltar ga Kwamitin masu Safara, da Gwamnatin Jihar Katsina da Kuma EMOG.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng