Maggi Ajinomoto babbar annoba ne ga lafiyar al'umma

Maggi Ajinomoto babbar annoba ne ga lafiyar al'umma

- An hana amfani da maggin Ajinomoto a kasar Pakistan

- Masana sun tabbatar da cewar maggin yana da babbar ila ga kwakwalwar mutum

- An haramta yin amfani da maggin a kasashe da dama ciki kuwa harda kasar Amurka

Maggi Ajinomoto babbar annoba ne ga lafiyar al'umma
Maggi Ajinomoto babbar annoba ne ga lafiyar al'umma

Kasar Pakistan ta haramta yin amfani da Ajinomoto ko gishirin china, wanda a turance ake ce ma Monosodium Glutamate saboda yana da illa ga kwakwalwar mutun.

DUBA WANNAN: NNPC: Najeriya tana sarrafa kowanne gangar mai akan Dala 20

Kasar ta yi hanin ne a jahohi 4 da garuruwa 3 masu zaman kansu, hakan ya fito ne daga babbar kotun kasar ta Pakistan.

Al’umma na amfani da gishirin don kara wa abinci dandano, ba ma kamar kashen gabashin Asiya. Kwarrarun likitoci sun bayyana cewar ya na da illa matuka ga jijiyoyin kwakwalwar mutum.

An sanya dokar ta hana amfani Ajinomoto cikin abincin jarirai da basu wuce wata 3 ba a kasar turai, da kuma rage yawan sanya shi a abinci a wasu kasashe 50 wanda suka hada da Amurka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng