Babu wani haraji da muka karawa masu ibada - Saudiyya
Hukumar aikin Hajji da Umara na kasar Saudiyya ta yi watsi da rade-raden cewa gwamnati na shirin sanya kudade na daban ga mahajatta da masu umara da suka daga kasashen ketare.
Jaridar Almadina da ake wallafawa da harshen larabci ce ta fara wallafa labarin a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu.
Hakan ya biyo bayan jita-jita da aka wallafa a shafukan zumunta cewa gwamnati za ta karbi Riyal 400 zuwa 700 ga duk wanda ya shigo kasar dan yin ibada da shekarunsa suka darawa 18.
Kuma wai ma'aikatar aikin hajji da umarar za ta kafa wasu cibiyoyi a filayen jiragen kasar da cikin birnin Makka dan karbar kudaden a hannu mutanen.
KU KARANTA KUMA: Zamu karfafa hukumomin gargajiya domin magance rikin makiyaya da manoma
Gwamnatin ta tabbatar da babu wannan batun sam, amma ta na shirin sake fadada girman wuraren da Alhazai za su zauna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng