'Dan kunar bakin wake ya kashe jami'an tsaro 3, ya kuma raunana mutum 17 a Borno
- Wani dan kunar bakin wake ya yi sanadiyar mutuwa Sibiliyan JTF 3 da raunana wasu mutane 17 a jiha Borno
- Lamarin ya faru ne a daren jiya bayan dan kunar bakin waken ya shigo garin a kan keke inda ya ratsa inda mutanen suke kafin ya tayar da bam din
- Jami'an yan sanda sun ziyarci inda abin ya faru, sun kuma garzaya asibiti da wanda suka sami raunuka don karbar jinya
Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a garin Muna-Datti da ke karamar hukumar Jere na Jihar Borno inda ya hallaka jami'an tsaron farar kaya wato 'Civilian JTF' gida uku da kuma raunana mutane 17.
A sanarwan da ya aike wa jaridar Leadership, mai magana da yawun rundunar yan sanda na Jihar Borno, DSP Joseph Kwaji ya ce tuni an kwashe gawawakin wanda suka rasu tare da wanda suka jikkata zuwa Asibitin koyarwa na Jami'an Maiduguri.
KU KARANTA: Ya yi ikirarin Allah ne ya aiko shi saboda irin mu'ujizar da yake nunawa
"A ranar 05 ga watan Maris misalin karfe 8.30 na dare, Wani dan kunar bakin wake da ya taho kan keke dauke bam ya fasa bam din a unguwar Muna Datti inda ya kashe kan sa tare da halaka wasu jami'an Civilian JTF guda 3. Wasu mutane 17 sun sami raunuka kuma tuni jami'an yan sanda sun ziyarci wurin.
"An kwashe gawawakin wanda suka rasu tare da wanda suka sami raunuka zuwa asibitin koyarwa na Maiduguri. A halin yanzu al'umma sun fara cigaba da harkokin su, inji DSP Kwaji.
Kwanakin baya, kwamishinan yan sanda, Damian Chukwu ya bayyana cewa hare-haren da ke afkuwa a yankin na Muna ya na da nasaba da dimbin yan gudun hijira da suka tare a garin duk da cewa an sharce su da su koma gidajen su. Hakan ne ya bawa yan ta'adda damar shigowa garin suna aikata barnar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng