‘Yan Makarantar Dapchi: Shehu Sani ya ce da yaran manya ne da sun dawo gida

‘Yan Makarantar Dapchi: Shehu Sani ya ce da yaran manya ne da sun dawo gida

- Sanata Shehu Sani ya bayyana abin da ya saka gagara ceto Matan Dapchi

- Kwamared Sani yace da ace yaran mala’u ne da tuni an gano su a yanzu

- Tun kwanaki aka kara sace wasu ‘Yan makaranta a Garin Dapchi a Yobe

Mun samu labari cewa Sanatan Jihar Kaduna Kwamared Shehu Sani ya kuma caccakar Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da ‘Yan matan da aka sace kwanan nan a Garin Dapchi.

‘Yan Makarantar Dapchi: Shehu Sani ya ce da yaran manya ne da sun dawo gida
Ana zargin 'Yan Boko Haram da sace ‘Yan Makarantar Dapchi

Sanatan na Jihar Kaduna ta tsakiya yayi tir da satar ‘Yan makarantar Gwamnatin da aka yi a Jihar Yobe a makonnin da su ka wuce. Sanatan Kasar yace da ace Yaran manya ne aka sace a makaranta da tuni an yi wuf an nemo su.

KU KARANTA: Shugaban Hafsun Sojin Najeriya yace za su ga karshen ta'addanci

Kwamared Sani yake cewa ba a maida hankalin da ya dace ba wajen ceto yaran don kuwa ba ‘Ya ‘Yan Gwamnoni, Sanatoci ko Ministoci da ma Sarakunan gargajiya bane. Har yanzu dai da ake magana babu labarinb yaran.

A baya dai Sanatan yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara inda wannan abu ya faru. Daga dai jiya mu ka ji cewa Shugaban kasar ya fara kai ziyara domin ganewa kan sa da kan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel