Likitocin Saudiyya sun warkar da makafi 515 a Garin Kano

Likitocin Saudiyya sun warkar da makafi 515 a Garin Kano

- Wasu Likitoci sun warkar da makafi da dama a Garin Kano

- Makafi sama da 515 su ka dawo gani ran-ga-da-dau a yanzu

- Kungiyar Musulman Matasan Duniya ta dauki wannan nauyi

Wasu Likitocin Kasar Saudiyya karkashin wata Kungiyar Matasa ta Duniya da kuma hadin kan Hukuma ta gudanar da aiki kyauta ga masu ciwon ido a Jihar Kano.

Likitocin Saudiyya sun warkar da makafi 515 a Garin Kano
Saudi tayi wa masu fama da makanta magani a Kano

Wasu taron Likitoci wanda su ka kware a harkar gyaran idanu har 5 tare da hadin-gwiwar Kungiyar Musulman Matasa ta Duniya baki daya ta duba masu fama da larurar idanu har mutane sama da 500 a cikin Jihar Kano.

KU KARANTA: Manyan 'Yan siyasa za su sauya sheka a Najeriya

Wani Babban Jami’in Kasar Saudi Yousef Ibrahem Alghamdi ya bayyana cewa sun yi mutane 515 gyara a idanun su a Garin Kano. Wasun su dai har sun samu karamar makanta wanda yanzu sun dawo su na gani radau.

Ibrahem Alghamdi yace rashin hali ya hana wadannan Bayin Allah su samu waraka don haka aka dauki nauyin su. Bayan yi masu aiki a idanun an kuma cigaba da ba su magunguna kyauta domin ganin sun wartsake gaba daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel