Na kasa gane abunda Buhari ya je yi a bikin Kano alhalin har yanzu ba’a ga yan mata 110 ba – Bakare
- Fasto Bakare ya caccaki shugaba Buhari da gwamnoni 22 da su je Kano domin auren yar Ganduje
- Faston yace zuwa bikin aure bayan yan Boko Haram sun sace yan matan makarantar Dapchi da kuma kashe masu bayar da agaji na majalisar dinkin duniya ya nuna cewa shugabannin basu da tunani
- Ya yi tambayan ko zasu halarci biki da ace akwai daya daga cikin yayansu a wadanda aka sace a Dapchi
Fasto Tunde Bakare, shugaban cocin Latter Rain Assembly (LRA), ya ce ya rasa gane mai shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 22 ke yi a bikin Kano, yayinda har yanzu ba’a saki yan mata 110 na Dapchi ba.
A ranar Asabar, 3 ga watan Maris, akalla gwamnoni 22 suka ziyaarci Kano, domin murnar auren Idris Ajimobi da Fatima Ganduje, yayan Abiola Ajimobi da kuma Umar Ganduje, gwamnonin jihohin Oyo da Kano.
Haka zalika wadanda suka halarci bikin sun hada da shugaban kasa da kuma manyan mambobin jam’iyyar APC, ciki harda Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagas.
Bakare yace zuwa bikin aure bayan yan Boko Haram sun sace yan matan makarantar Dapchi da kuma kashe masu bayar da agaji na majalisar dinkin duniya ya nuna cewa shugabannin basu da tunani, jaridar Cable ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Daga Dapchi zuwa Chibok: Sabuwar Wasikar Reno Omokri ga Lai Mohammed
Da yake Magana a cocin sa a a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris, Bakare yace duk wanda ya san gaskiyar haalin da abubuwa ke cioki a Najeriya zai yi ma kasar kuka.
Daga karshe Ya yi tambayan ko zasu halarci biki da ace akwai daya daga cikin yayansu a wadanda aka sace a Dapchi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng