Wani Yaro ya shiga uku bayan an yi ram da shi yana karya da sunan Sarkin Kano
- ‘Yan Sanda sun kama wani Matashi da ke karya da sunan Sarkin Kano
- Sultan Bello ya bude shafin Instagram na Mai Martaba Sarki Sanusi II
- Ana zargin Saurayin da damfarar jama’a kudin da ya haura Miliyan 3
Mun samu labari cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun fara binciken wani yaro mai shekaru 20 a Duniya da ya ke karya da sunan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a kafar zamani na Instagram.
Jami’an tsaron kasar sun yi ram da wannan Matashi mai suna Sultan Bello yana karya da sunan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a shafin sadarwa na zumunta na Instagram inda har ya tara dinbin mabiya wanda su ka dauka Mai Martaba ne da gaske.
KU KARANTA: An kashe mutum bayan an aiki hari a kusa da fadar Amurka
DSP Magaji Majiya wanda ke magana da yawun bakin ‘Yan Sandan Najeriya a Kano ya bayyana cewa Sultan Bello ya shiga hannu ne bayan wata mata ta fallasa shi. Wannan yaro ya damfari mutane ta hanyar turo masa miliyoyin kudi a asusun sa da sunan Sarki.
Wannan saurayi dai yanzu yana hannun hukuma inda aka yi kira ga matasa da su guji irin wannan danyen aiki. A baya dai Sarkin ya taba bayyana cewa ba ya amfani da irin wadannan shafuka na zamani amma tuni har Instagram ta tantance lambar karyar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng