Rundunar 'yan sandan Zamfara ta dakile yunkurin kai hari a Anka

Rundunar 'yan sandan Zamfara ta dakile yunkurin kai hari a Anka

- ‘Yansandan jihar Zamfara sun samu nasarar dakile harin da wasu gungun 'yan bindiga suka shirya kai wa garin Anka

- Gwamnatin jihar Zamfara ta ce 'yan bidiga sun kashe mutane 1,321 tun daga shekara 2011 zuwa yanzu

Hukumar rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta ce jami’an ta sun dakile harin da wasu gungun ‘yan bindiga suka shirya kai wa karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Kakakin rundunar ‘yansadar jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya bayyana haka a birnin Gusau, inda ya ce, jami’an su sunyi musayar wuta da wasu ‘yanbindiga da akan babura kafin suka tsere cikin daji.

Rundunar 'yan sandan Zamfara ta dakile yunkurin kai hari a Anka
Rundunar 'yan sandan Zamfara ta dakile yunkurin kai hari a Anka

Yace, ‘jami’an su sun yi nasarar kama daya daga cikin ‘yan bidigan, tare da kwace muggan makamai daga hannunsa.

KU KARANTA : Dokar kashe masu yada kalaman batanci: Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kaca-kaca da majalissar dattawa

Wani rahoto da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar ya nuna cewa daga shekara 2011 zuwa yanzu, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 1,221 yayin da suka jikkata mutanen 1,781.

Kakakin majalisar dokokin na jihar Zamfara, Alhaji Sanusi, ya ce 'yan bindiga sun sace shanu akalla 8,000 da lalata gonaki da kuma rusa gidaje 9,000 tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng