An soki Shugaba Buhari na zuwa biki a maimakon ziwa jaje a Yankin Boko Haram
- An yi Allah-wadai da Shugaba Buhari na zuwa taron biki a Kano
- A makon nan ne Fatima Ganduje ta auri sahibin ta Idris Ajimobi
- ‘Yan Boko Haram sun yi barna Shugaban kasar bai kai ziyara ba
Mun fahimci cewa Jama’a da dama sun soki Shugaba Muhammadu Buhari na zuwa biki a Jihar Kano a maimakon zuwa jaje a Yankin da rikicin Boko Haram ya auka masu cikin ‘Yan kwanakin nan. Haka dai aka yi a lokacin tsohon Shugaba Jonathan Goodluck.
Yanzu haka dai ana fama da rikicin ‘Yan Boko Haram ne a Jihohin Arewa maso gabas musamman Yobe da Borno amma Shugaba Buhari ya wuce bikin ‘Ya ‘yan Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma na Gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi.
KU KARANTA: Da-dumi: An kai hari a fadar Shugaban kasar Amurka
Wata Hadimar Shugaban kasar Lauretta Onochie ta gamu da fushin jama’a lokacin da ta tace Shugaba Muhammadu Buhari na da damar kai ziyara duk inda ya ga dama a kasar. Hakan dai bai yi wa har magoya bayan Shugaban kasar dadi ba.
Kwanan nan aka sace ‘Yan mata sama da 100 a Garin Dapchi yayin da ‘Yan Boko Haram su ka kai mummun hari a Garin Rann inda ta kai masu bada taimako su ka fara tsere daga Garin. Shugaban dai ya zabi taron biki a madadin ya kai ziyara wadannan wurare.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng