Harin da yan Boko Haram suka kaiwa yan agaji a Rann, jihar Borno ya nuna cewa babu Allah a zukatansu
- Shugaban kasa Buhari yayi Allah wadai da harin da aka kaiwa yan agaji a Rann, jihar Borno
- Ya ce harin ya nuna karara cewa yan ta’addan Boko Haram basu da tsoron Allah
- Buhari ya kara da cewa babu wani addinin gaskiya da ya yarda da zaluntan bayin Allah
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace harin da aka kaiwa ma’aikatan dake bayar da agaji a Rann, jihar Borno, ya nuna karara cewa yan ta’addan Boko Haram basu da tsoron Allah, imani sannan sun cancanci a yi watsi dasu.
"Kamar yadda nake fadi a koda yaushe, babu addinin gaskiya da ya yarda da zaluntan bayin Allah. Kai hari da kahe wadanda ke bayar da agaji ga al’umma ya nuna tsangwaran rashin imani. Abun ki ne a wajen Allah da ma mutane.” Cewar shugaban kasar yayinda yake ta’aziyya ga majalisar dinkin duniya da sauran hukumomin bayar da agaji dake aiki a Rann, da kuma kasar baki daya.
Shugaban kasa Buhari ya ba da tabbacin cewa irin wannan harin zai karfafa gwiwar gwamnati ne wajen kawo karshen yan ta’addan Boko Haram, a dan kankanin lokaci.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Zamfara ta nada Dan Ali a matsayin sabon sarkin Birnin Magaji
A baya Legit.ng ta rahoto cewa harin ya afku ne “bayan duhu” a wajen wani sansani dake dauke da mutane 55,000 da rikicin ya sa suka zama masu gudun hijira.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng