Gwamnatin Zamfara ta nada Dan Ali a matsayin sabon sarkin Birnin Magaji

Gwamnatin Zamfara ta nada Dan Ali a matsayin sabon sarkin Birnin Magaji

Bayan mutuwar sarkin Birnin Magaji, Alhaji Ahmad Umar Usman, cikin gaggawa gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da nadin Alhaji Ibrahim Muhammad a matsayin sabon sarki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kwamishinan kasafin kudi da shirin tattalin arziki, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 1 ga watan Maris.

Legit.ng ta tattaro cewa a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu ne, sarkin Birnin Magaji, Alhaji Ahmad Umar Usman ya rasu bayan yar gajeruwar jinya da yayi a asibitin Gusau.

Sabon sarkin, mai shekaru 51 da haihuwa, ya kasance mai bada shawara na musamman ga ofishin mataimkin Gwamna tsakanin 2011 da 2015.

Ya kuma rike mukamin mataimaki na musamman ga ministan tsaro kafin sabon nadi na kwanakin nan.

KU KARANTA KUMA: Buhari na aiki domin ganin an karyar da farashin shinkafa ga yan Najeriya - Bagudu

Dan Ali ya halarci taron makarantun firamare Birnin Magaji inda ya cigaba da karatu a makarantar Sakandare, Kaura Namoda.

Ya halarci kwas da dama a cibiyoyin makarantun tarayya har da jami’an Jos, jihar Filato. Ya kasance mai mata daya da yara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng