Kujerar Shugaban kasa ba ta yaro ba ce – Inji Sheikh Dr. Pantami
- Ana neman Shugaban NITDA Dr. Isa Ali Pantami ya tsaya takara
- Babban Shehin Addinin Musuluncin yace kujerar tayi masa girma
- Jama’a da dama sun yaba da kokarin Pantami a Hukumar NITDA
Mun samu labari cewa Shugaban Hukumar NITDA ta Najeriya Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami yayi magana game da kiran da ake yi masa na ya tsaya takarar Shugaban kasa a nan gaba.
Babban Malamin Addinin kuma kwararre a harkar sha’anin Boko ya samu lambar yabo ne daga Jama’a bayan irin kokarin da aka ga yana yi a Hukumar NITDA. Sai dai Dr. Pantami yana ganin kujerar Shugaban kasa ta fi karfin sa.
KU KARANTA: Sai yanzu Najeriya ta dawo daidai bayan na karbi mulki
Wani Bawan Allah mai suna Ibrahim Sani yace zai so ya ga irin su Sheikh Dr. Is Pantami rike da mulkin kasar nan. Sani yace burin sa a samu mutane irin su Isa Pantami su mulki Najeriya don kuwa Malamin ya san hakkin al’umma.
Shi dai babban Malamin yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda ya bayyana cewa kujerar tayi masa nisa amma dai ya gode da irin shaidar da aka yi masa. Kwanaki an nemi Shugaban na NITDA ya fito takarar Gwamnan Jihar Gombe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng