Gamayyar kungiyar matasan Arewa (ACF) sun yi kira ga Buhari ya sanya dokar ta baci a jihar Zamfara
- Kungiyar matasan Arewa sun ce shugaba Buhari ya sanya dokar ta bacci Zanfara
- Kungiyar ACF ta ce gwamna Abdul Aziz Yari ya gaza wajen kare rayukan mutanen jihar Zamfara
Gamayyar kungiyar matasan Arewa (ACF), sun yi kira da babban murya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gaggauta sanya dokar ta baci a jihar Zamfara.
Sun ce gazawar gwamnan Jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari, wajen kare da dukiyoyi da rayukan al’ummar jihar ya sa suka yi wannan kiran.
Mai magana da yawun bakin kungiyar, Malam Abdul Azeez Suleiman, ya bayyana haka ne a lokacin taron manema labaru a jihar Kaduna.
Matasan sun ce halin ko in kula da gwamnan Jihar Zamfara, Abdulazeez Yari, yake nunawa akan halin da Jama’ar jihar suke ciki abun takaici ne da damuway.
KU KARANTA : Rikicin Adamawa : An kashe kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamwa - PDP
A lokacin da al’ummar jihar suke fama da kashe kashe da zubar da jini, gwamnan ya mayar da hankalin shi wajen tafiye tafiye da sharholiya a kasashen waje.
Kungiyar matasan sun ce hakika gwamnan, Abdul’aziz Yari da ‘yan Majalisar jihar, sun gaza matuka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng