Kudurin kirkirar Peace Corps: Majalisar wakilai ta yi alla-wadai da kin amincewar Buhari

Kudurin kirkirar Peace Corps: Majalisar wakilai ta yi alla-wadai da kin amincewar Buhari

- Wani dan majalisar wakilai ya ce zai jagoranci zanga-zangar don nuna kin amincewa da watsin da shugaba Buhari ya yi da batun kirkirar Peace Corps

- Dan majalisar, dan asalin jihar Delta, ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya hangi kudirin ta fuskar samar da aiki ga matasa

- Wani mamba a majalisar daga Dapchi ta jihar Yobe ya goyi bayan dan majalisar

A jiya ne wasu mambobin majalisar wakilai sun bayyana adawar su da watsin da shugaba Buhari ya yi da kudirin kirkirar Peace Corps.

Mambobin majalisar sun bayyana cewar kin amincewar Buhari zai dagula lamuran tsaro a kasar nan.

Majalisar Wakilai ta nuna rashin jin dadin ta bisa yadda Buhari ya ki amincewa da kudirin Peace Corp
Majalisar Wakilai ta nuna rashin jin dadin ta bisa yadda Buhari ya ki amincewa da kudirin Peace Corp

Da yake tsokaci a kan kin amincewar Buhari, Nicholas Ossai, daga jihar Ribas, ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya kalli abin ta fuskar samar da aiki ga matasa.

DUBA WANNAN: An gurfanar da 'dan tsohon gwamna gaban kotu bisa almundahanar biliyan N1.5bn

Ossai ya bukaci majalisar ta yiwa batun watsin da Buhari ya yi da kudirin peace duba na tsanaki.

Kazalika mamba a majalisar, Goni Bukar Lawan, daga jihar ya bayyana cewar kin amincewar Buhari na shine ke nufin batun kirkirar Peace Corps ya mutu murus ba.

Wani dan majalisar daga Dapchi ta jihar Yobe ya ce da akwai hukumar tsaro kamar Peace Corps da ba'a sace 'yan matan Dapchi a makarantar da su ke karatu ba.

Legit.ng ta rawaito maku a daya daga cikin labaran ta cewar shugaba Buhari ya ki amincewa da bukatar majalisun kasar nan na kirkirar Peace Corps a matsayin sabuwar hukumar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel