Masu garkuwa da mutane sun fitini al’ummar Jihar Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun fitini al’ummar Jihar Kaduna

- Masu garkuwa da mutane sun sace Uwargidar wani Bawan Allah jiya

- A cikin daren jiya aka sace Iyalin Nasiru Yakubu a Garin Birnin Yero

- Nasiru Yakubu babban ‘Dan Jarida ne da ke aiki da VOA na Amurka

Mun samu labari cewa a jiya da dare ne wasu ‘Yan bindiga su ka shiga wani Kauye a kan hanyar zuwa Garin Kaduna inda su ka sace wata mata da ‘dan ta. An rasa ran mutum guda a wannan hari da aka kai cikin dare.

Masu garkuwa da mutane sun fitini al’ummar Jihar Kaduna
'Yan bindiga sun shiga Garin Birnin Yero a Jihar Kaduna

Wannan mummunan abu ya faru ne kimanin karfe 1:30 na tsakar dare inda masu garkuwa da mutane su ka dura Garin Birnin Yero su ka yi gaba da mai dakin wani ma’aikacin gidan Jaridar VOA ta Amurka da kuma wani yaron ta har su ka harbe wani.

KU KARANTA: Rikicin Jihar Kaduna yayi mugun naso

Nasiru Yakubu ya bayyanawa Jama’a wannan cikin dare bayan faruwar wannan abu inda ya nemi addu’a daga Jama’a. Legit.ng Hausa ta zanta da mutanen garin wadanda su ka tabbatar da cewa sun ji harbi a cikin dare yayin da abin ya faru.

A kwanakin baya ma dai masu garkuwa da mutanen sun shigo wannan Gari na Birnin Yero inda su ka sace wata mata har sai da aka biya kudi har Naira Miliyan daya da ‘yan kai. Nasiru Yakubu yana aiki ne a gidan Rediyon VOA Hausa da Nagarta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng