Yan fashi sun kai harin bazata ga yan kasuwa a Zamfara, 3 sun bata

Yan fashi sun kai harin bazata ga yan kasuwa a Zamfara, 3 sun bata

Wasu da ake zargin yan fashi da makami ne sun kai harin bazata ga motocin yan kasuwa dake hanyar zuwa garin Dansadau a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara, cewar daya daga cikin wanda abun ya shafa.

An tattaro cewa yan kasuwan na hanyar komawa gida daga birnin Kano tare da kayayyakinsu lokacin day an fashin suka bude masu wuta tsakanin Hannu Tara da kuma kauyen Mashayar Zaki kusa da Dansadau.

Wani dan kasuwa dake samun kulawar likita sakamakon harbinsa da akayi ya bayyana cewa sai da suka tsaya a Magami saboda duhu sannan washegari suka tafi Dansadau, amma sai yan fashi suka far masu.

Yan fashi sun kai harin bazata ga yan kasuwa a Zamfara, 3 sun bata
Yan fashi sun kai harin bazata ga yan kasuwa a Zamfara, 3 sun bata

Ya ce yan fashin sun bukaci daya daga cikin yan kasuwar da su fara sauke kayayyakin zuwa motocinsu, don haka dole ya bi abunda suka ce, daga bisani suka yi masu mugun duka.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Ana shirin maka Ganduje a kotu

Ya ci gaba da cewa basu san inda mutane uku suka shiga ba; ciki harda wata mata, sannan kuma cewa kimanin su takwas ke kwance a asibiti a yanzu.

Ba a samu kiran kakakin yan sandan jihar, DSP Muhammad Shehu ba a lokacin kawo wannan rahoton.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng