Hukumar JAMB ta gargadi iyaye da su kauracewa cibiyoyin da ake rubuta jarabawar JAMB
- Hukumar JAMB ta ce bata son ta ga iyayen dalibai a duk wani cibiyar rubuta jarabawar JAMB
- JAMB ta ce iyaye suna zuwa wurin rubuta jarabwar JAMB ne dan ba wa yaran su satan amsa
Hukumar rubuta jarabawar shiga jami'a da kwalejojin ilimi (JAMB) ta gargadi iyayen daliban da za su rubuta jarabawar JAMB na shekara 2018 da su kauracewa cibiyoyin rubuta jarabawar JAMB.
Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja a lokacin da yake bibiyar jarabawar gwaji da hukumar ta gudanar a cibiyar gudanar da jarabawar JAMB dake jami’an Kogo da Veritas.
Ya ce wasu iyaye suna da dabi’ar zuwa wurin rubuta jarabwar JAMB dan ba wa 'ya'yan su satan amsa.
KU KARANTA : Dattawan yankin Kudu da na Arewa ta tsakiya sun gargadi Buhari akan sanya dokar ta baci a jihar Benuwe
Ya ce, “Muna rokon iyaye da su kauracewa duka cibiyoyin rubuta jarabawar JAMB, muna shirya yaran nan ne dan shiga jami'a da kwalejojin ilimi, amma sai iyayen su rika zuwa wurin gudanar da jarabawar.
"Suna son ‘ya’yan su su ci jarabawar ta kowani hali, wani dabi’a ba zai taimaki ‘yayan su ba, saboda ba za cigaba da bin yaron su zuwa lacca a jami’a ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng