Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna (hotuna)

Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna (hotuna)

A daidai lokacin da yan fim suka yi kaurin suna wajen rashin auren junansu dama rashin zaman aure musamman a tsakanin matansu, wadannan jarumai biyu sun kafa tarihi wajen karyata wannan hasashe.

Ma’aurata sannan kuma masu fada aji a masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Muhibbat Abdulsalam da angonta babban darakta Hassan Giggs sun nuna irin tarin soyayya da kaunar da suke ma junansu.

A koda yaushe ma’auratan kan yi kokarin nunawa duniya irin kaunar da suke ma junansu wanda hakan ne ya sa suke burge mutane.

Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna (hotuna)
Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna

Hassan Giggs yana mai godiya da farin ciki samun matar kamar Muhibbat wacce ta kasance tsohuwar jaruma a masana’antar fim.

"Kyuata mafi soyuwa da zaka baiwa yaran ka shine kia so mahaifiyar su. Alhamdulillah da samun wannan kyautar a rayuwa ta" jarumin ya wallafa a shafin sa na Instagram.

Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna (hotuna)
Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna (hotuna)

Shekara goma kenan da auren su wanda Allah ya albarkace su da yara mata su uku Humaira, Azeema da Khadijah.

BKU KARANTA KUMA:

A baya Legit.ng ta kawo inda daya daga cikin sabbin fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood da ke da hedikwatar ta a garin Kano mai suna Halima Ibrahim ta siffanta masana'antar da wata makaranta dake cike da darussa da dama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng