Da kamar wuya: Sulhunta El-Rufai da Shehu Sani zai yi wuya saboda wasu hujjoji muhimmai guda 4
A ranar Lahadi, 25 ga watan Feburairu ne tsohon gwamnan jihar Ekiti, kuma mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Segun Oni ya isa jihar Kaduna don duba yiwuwar dinke baraka dake tsakanin Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai da Sanata Shehu Sani.
Sai dai masu bibiyan siyasar jihar na ganin da kamar wuya, wai an ce a dafa kaza a yar, bisa wasu dalilai kamar haka:
KU KARANTA: IBB da Obasanjo na bakin ciki da nasarorin da Buhari ya samu ne – Sanata Kurfi
Biyayya: A yayin da jam'iyyun CPC, ACN, ANPP da wani bangare na APGA suka dunkule a shekarar 2013, suka kafa jam'iyyar APC, ya kasance dukkanin bangarorin sun shigo ne a matsayin sa'annin juna. Da Wannan idanu El-Rufai da Shehu Sani suke kallon juna, babu wani Maigidan wani, kuma babu yaron wani a tsakaninsu.
Wannan kallon biri da ayaba dake tsakanin yan siyasan biyu ya cigaba har bayan da El-Rufai ya lashe zaben gwamna, inda aka yi tsammanin Sanatan zai yi ma sa biyayya a matsayinsa na shugaba a jihar Kaduna, amma Ina.
Masu bibiyan Al'amuran siyasar Kaduna na ganin matukar ba wai Sanatan ya baiwa gwamnan girmansa ba, sulhu haihata haihata
2019:
Wani muhimmin dalili da zai kawo ma kokarin sulhunta El-Rufai da Kwamared tasgaro shi ne 2019.
Sanannen abu ne cewa yan siyasa sun wasa kubensu don samun nasara a zabukan 2019, musamman a Kaduna, inda gwamna El-Rufai yake goyon bayan hadiminsa, Uba Sani a don taka takarar mukamin Sanatan Kaduna ta tsakiya, kujerar da Shehu Sani ke danawa.
Da wannan ne yasa ake ganin ko da Shehu Sani ya bada kai bori ya hau, na ganin an sulhunta shi da gwamnan, ba zata canza zani ba, sai sun yi kokarin karya shi a 2019.
Mukamai:
Tun farin gwamnatin gwamna El-Rufai a lokacin da dangataka ta yi tsami a tsakaninsa da Shehu Sani ne ake danganta rikicinsu da rashin baiwa jama'an Sanatan mukamai a gwamnatinsa.
Dukkaninsu sun tabbatar da hakan a lokutta daban daban, inda Sanatan ya koka kan cewa an nemi sunayen wadanda za'a baiwa mukamai a hannunsa, ya tura, amma aka yi watsi da nasa.
Sai dai gwamnan ya tabbatar da hakan, amma yace mutanen da Sanatan ya turo masa basu da kwarewa tare da karancin ilimi.
Don haka indai ba gwamnan ya ja da baya ya shigar da mutanen Shehu Sani gwamnati ba, wanda babu wani alamu zai yi hakan, toh sulhu ba zai yiwu ba.
Buhari:
Kyakkyawar alaka da dangantaka dake tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da El-Rufai ba boyayyen abu bane, wanda hakan bai yi ma abokan hamayyarsa dadi ba, musamman masu ganin saboda Buhari El-Rufai ya ci zabe.
A cewar masana, wannan alaka tsakanin Buhari da El-Rufai na ci ma Sanata Shehu tuwo a kwarya, kamar yadda aka saba ganinsa yana sukar alakar tasu.
Da wannan ne ake ganin kwamitin sulhun da Buhari ya kafa a karkashin jagorancin Tinubu, ba zai taka rawar gani ba a jihar Kaduna, ma'ana aikin gama ya gama a Kaduna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng