Jami’an Yansanda sun bindige masu garkuwa da mutane yayin musayar wuta a Zamfara

Jami’an Yansanda sun bindige masu garkuwa da mutane yayin musayar wuta a Zamfara

Rundunar Yansandan jihar Zamfara ta sanar da hallaka wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara, tare da kama mutum takwas da kuma kwato tarin makamai.

Kwamishinan Yansandan jihar, Kenneth Embrimson ne ya ne ya bayyana haka yayin da yake bajakolin gawar shugaban yan ta’addan, a garin Gusau, inda ya shaida ma yan jaridu cewar ya mutu ne a sakamakon musayar wuta da yansanda.

KU KARANTA: IBB da Obasanjo na bakin ciki da nasarorin da Buhari ya samu ne – Sanata Kurfi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan na fadin sun samu rahoton yan bindigan sun dira kauyukan Ruwan-gizo da Yartasha, dake karamar hukumar Talatar mafara, inda suka saci wani mutumi mai suna Bilyaminu Abdullahi.

“Ba tare da bata lokaci ba, muka shirya musu tarkon rago, inda muka kwashe awanni musayar wuta na tsawon awanni biyu, har sai da muka kwato Bilyaminu, tare da kashe shugabansu, sa’annan muka jikkata da dama. Mun kwato bindigu kirar AK 47 guda biyu, alburusai da Babura guda biyu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, kwamishina Embrimson yay ace Yansanda sun kama wasu masu garkuwa da mutane su biyu a ranar 24 ga watan Feburairu, a kauyen Daraga da Dankurmi dake karamar hukumar Maru, haka zalika sun kama wasu su biyar a kauyen Magarya, dake garin Zurmi.

Bugu da kari, Kwamishinan yace sun sake kama wani mai garkuwa da mutane da wani dan fashi a kauyukan Kabala da Yan galadima duk a cikin karamar hukumar Maradun, duk a cikin aikin nasu sun kama wani mai karbar ma barayin mutane kudin fansa dauke da kudi naira miliyan 2.6.

Daga karshe Kwmamishina Kenneth Embrimson ya shawar jama’a da su cigaba da yansanda hadin kai tare basu bayanan sirri don kawar da masu aikata miyagun ayyuka a tsakanin al’umma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng