Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin malaman jami’ar Maiduguri da Boko Haram ta saki
Malaman jami’ar Maiduguri uku da mace daya da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka saki kwanan nan sun gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadan shugaban kasa da ke Abuja.
Wadanda ke ganawa da shugaba Buhari sune jami’ar yan sanda da kuma iyalan wata yar sanda da ta mutu yayin wannan iftila’i.
Zaku tuna cewa yan Boko Haram sun sace malaman jami’ar Maidguri 3 a Magumeri, jiha Borno yayinda sukaje hakan man fetur, su kuma jami’an yansanda a Damboa, Maduguri.
An sako su ne bayan wani ciniki da akayi tsakanin yan Boko Haram da gwamnatin tarayya ta kungiyar Red Cross.
Amma wani sanata mai wakiltar mazabar Gombe ta kudu, Joshua Lidani, ya soki yadda gwamnatin tarayya ke biyan yan Boko Haram domin sakin wadanda suka sace.
KU KARANTA: Jami’an hukumar kwastam suna sumogan shinkafa da motoci a farashin N30,000 a iyakokin kasar
Ya bayyana cewa wannan abu ke sanyasu suke cigaba da garkuwa da mutane a yankin arewa maso gabashin tarayya.
Yayi wannan jawabi bayan yan Boko Haram sun sake garkuwa da dalibai mata 110 a makarantan Dapchi da ke jihar Yobe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng