Wasu Matasan PDP a Kano sun sabunta kiran Kwankwaso ya bar APC
- Ana cigaba da kira ga Rabiu Kwankwaso ya tattara ya bar APC
- Su na so a hada kai a tika Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kasa
- Tsohon Gwamna Shekarau su ne manya a Jam’iyyar PDP a Kano
Mun samu labari na musamman cewa wasu Matasa da ke bayan Jam'iyyar PDP a Jihar Kano sun yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar kuma Jagoran su Sanata Rabi’u Kwankwaso ya komo cikin Jam’iyyar PDP.
Wani Matashi a Garin Bachirawa da ke cikin Karamar Hukumar Ungogo mai suna Abba Yau Bachirawa ya bayyana mana cewa su na goyon bayan Sanatan Kano ta tsakiya Rabi’u Kwankwaso ya fice daga APC ya dawo cikin Jam'iyyar su ta PDP.
KU KARANTA: Ganduje yace Kwankwaso ba zai taba mulkin Najeriya ba
Wannan Matashi yace za su so ganin babban ‘Dan siyasar ya dawo Jam’iyyar sa ta asali watau PDP kuma su hada kai da ‘Yan cikin Jam’iyyar domin ganin an kauda Gwamnatin Ganduje saboda gazawar ta a fili wajen harkar ilmi da sauran su.
Matasan na PDP na ganin ya kamata tsofaffin Gwamnonin na Kano biyu watau Sanata Rabi’u Kwankwaso da kuma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau su hada kai wajen ganin sun kafa Gwamnati a 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng