Kwankwaso ya soki zaben kananan hukumomi na jihar Kano
Sanata mai wakiltar jihar Kano ta Tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya soki zaben kananan hukumomi na jihar Kano da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.
Sanatan ya bayyana cewa, zargin kananan yara da kada kuri'u a zaben kananan hukumomi na jihar ya faru ne a sakamakon jam'iyya daya kacal da tsaya takara a zaben.
Dangane da magudi da aka tafka a zaben, Kwankwaso ya bayyana cewa ya faru ne a sakamakon rashin tsayawa takara na sauran jam'iyyu.
Legit.ng da sanadin jaridar The Cable ta ruwaito cewa, hotunan kananan yara sun yadu a dandalan sada zumunta bayan gudanar da zaben a ranar 10 ga watan Fabrairu.
KARANTA KUMA: Jerin ƙasashe 10 mafi ƙanƙanta a fadin duniya
Sai dai a yayin mayar da martani, kwamishinan labarai na jihar Mohammed Garba ya bayyana cewa, wannan hotuna dai tun na zaben da ya wakana a 2015.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, 'yan sanda sun yi kacibus da wani mabaraci a kasar Sweden da tilin kudade da suka haura N270m.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng