Dapchi: Sojojin kasar Ingila za su taimaka wajen ceto daliban da aka sace
- Rundunar Sojin Ingila ta BMATT da ke Najeriya ta yi alkawarin taimakawa wurin kubutar da 'yammatan Dapchi
- Shugaban Rundunar, Manjo Ian Robertson, shi ne ya bayyana hakan jiya
- Ya kuma bayyana cewar samar da tsaro ga jinsin mata da kuma jin ta bakin su abu ne mai mahimmaci
Shugaban Rundunar Sojin Ingila ta BMATT da ke Najeriya, Manjo Ian Robertson, ya yi tir da hari da a ke zargin Boko Haram ta kai a makarantar 'yammata (GGSS) na garin Dapchi, Jihar Yobe, tare da sace wasu daga cikin 'yammatan.
Shugaban ya dau alkawarin Rundunar ta na da nufin taimakawa Hukumar Sojin Najeriya wurin kubutar da 'yammatan. Ya yi wannan bayani ne jiya a wani taro da a ka yi game da muryar mata a kan harkar tsaro. Ya ce rundunar ta na nan ta na lura da lamarin kafin ka shigo cikin sa.
KU KARANTA: Albishirin ku manoma: Kasashen Australia da Canada UAE su na bukatan doya 'yar Najeriya
Ya ce abun takaici ne yadda makarantun 'yammata ya zama wuri ma fi saukin kai hari. Bai dai yi magana kan yadda Gwamnatin Najeriya ta fuskanci lamarin ba, amma ya ce zai tabbata horon da rundunar na sa ke ba wa Sojin Najeriya bai nuna wariyar jinsi ba.
Ya kuma bayyana bukatuwar hobbasan Sojin Najeriya kan mata. Ya bayyana cewar daukacin Nahiyar Turai ta 'Europe', ta ba wa tsaro ga mata muhimmiyar mahimmaci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng