Oyegun zai goyawa Tinubu baya don sasantawa tsakanin 'yan jam'iyyar APC
- Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, John Odigie-Oyegun, ya yi alkawarin goyon bayan Tinubu game da sasantawa tsakanin 'yan jam'iyyar
- Ya yi wannan alkawari ne a wata wasika da ya rubuta da kan sa jiya zuwa ga Tinubu
- An aika kwafin wasikar zuwa ga Shugaban kasa da Mataimakin sa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisa
Ciyaman din jam'iyyar APC na Kasa, Cif John Odigie-Oyegun, ya yi alkawarin goyon bayan jagoran jam'iyyar na Kasa, Asiwaju Bola Tinubu, bisa aikin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba shi na sasantawa tsakanin 'yan jam'iyyar.
A wata wasika da Oyegun ya rubuta jiya da kan sa zuwa ga Tinubu, ya sakankance Tinubu zai iya sauke nauyin da Buhari ya dora ma sa. Ya kuma tabbatar ma sa da cewar zai goyi bayan sa ta ko wace hanya.
KU KARANTA: Labari mai dadi: Gwamantin tarayya ta bullo da shirin samar da ayyuka 500,000 daga fanin noma
Wasikar ta fito ne bayan Oyegun ya zanta da Shugaban Kasa Buhari a Fadar sa. An kuma mika kwafin wasikar ga Shugaban Kasa Buhari da Mataimakin sa Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa Saraki da kuma Kakakin Majalisar Dokoki Dogara.
Idan ba a manta ba, a ranar Laraba ne Tinubu ya rubuta wasika mai shafuka 7 ya na zargin Oyegun bisa korafi kan aikin da Shugaban Kasa ya ba shi na sasantawa tsakanin 'yan jam'iyyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng