Duk wanda ya sake rigima ko hayaniya a kaina ban yafe masa ba – Adam A Zango

Duk wanda ya sake rigima ko hayaniya a kaina ban yafe masa ba – Adam A Zango

Shahararren jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan Hausa kuma mawakin zamani, Adam Zango ya gargadi masoyansa kan maida martini mai ta da zaune tsaye kan wadanda ke aibata shi a shafukan zumunta.

Zango ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram inda ya ja hankalin masoyan nasa kan tayar da rigima.

Ya wallafa a shafinsa cewa: “DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI KO AN ZAGI IYAYENA A CIKIN KANNE NA, ABOKAINA DA YARANA….ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA”

Duk wanda ya sake rigima ko hayaniya a kaina ban yafe masa ba – Adam A Zango
Duk wanda ya sake rigima ko hayaniya a kaina ban yafe masa ba – Adam A Zango

KU KARANTA KUMA: Ku daina rayuwar takama – Sultan ga shugabannin addini

A kwanankin bayan nan ma an samucece-kuce tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu, inda Zango da magoya bayan Ali Nuhu suka dinga musayar yawu da mummunan kalamai, daga bisani ne manya suka shiga tsakani, har aka samu sulhu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng