Muna aiki tukuru don ganin fursunoni sun sami damar yin zabe a 2019 - INEC
- Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fara shirye-shiryen samar wa fursunoni damar kada kuri'a
- Hukumar INEc din ta nemi hadin kan Hukumar kula da gidajen yari na kasa NPS
- Dama tun a shekarar bara shugaban hukumar INEC ya yi alkwarin duba yiwuwar hakan
Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC ta tana duk mai yiwuwa don ganin cewa fursunoni sun samu damar kada kuri'ar su a babban zabe mai zuwa na 2019. INEC tana hadin gwiwa ne da Hukumar Kula da Fursunoni NPS don cinma nasara kafin zaben.
Babban sakataren INEC na jihar Kebbi, Alhaji Bello Magaji Isah ne ya bayar da sanarwan a yayin da ya ziyarci Kwantrola Janar na NPS, Mallam Sani Adamu a garin Potiskum na jihar kebbi.
DUBA WANNAN: Zan koma makaranta amma fa idan Buratai ne zai zama maigadin mu - Dalibar Sakandiren Dapchi
Alhaji Isah ya kara da cewa akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki don wayar da kan al'umma kan hakkin da wasu fursunonin ke dashi na kada kuri'a.
"Na zo nan ne don in sanar da ku cewa INEC na dubu yiwuwar bawa wasu daga cikin fursunoni daman kada kuri'a idan zabe ya zo." inji shi
A shekerar da ta gabata, Shugaban INEc na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar wa yan Najeriya cewa hukumar tana shirye-shirye don ganin cewa NPS za ta bawa wasu daga cikin fursunoni daman kada kuri'a idan lokacin zabe ya yi.
A jawabin sa, Shugaban NPS na jihar kebbi, Ja'afaru Ahmed ya umurci dukkan shuwagabanin gidajen fursuna na kasan nan su bawa hukumar INEC hadin kai don ganin cewa abin ya yiwu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng