Dandalin Kannywood: Zainab Indomie ta dawo bakin aiki
Shahararriyar jaruman nan da tauraronta ya walka a shekarun baya a dandalin shirya fina finan Hausa na Kannywood, wato Zainab Abdullahi wacce aka fi sani da Zainab Indomie ta yiwa masoyanta albishir.
Zainab ta bayyana cewa ta dawo bakin aiki domin jin dadin masoyanta da masu bibiyarta.
Jarumar wacce ta kwashe tsowon shekaru ba tare da anjin duriarta a masana'antar shirya fina-finai ta sanar da haka ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu a shafin ta na kafar sada zumunta ta Instagram.
KU KARANTA KUMA: Ba zamu iya ci gaba da wadannan munanan abubuwa ba – Sultan na Sokoto
Ta rubuta a shafinta kamar haka “Ina yiwa dukkannin masoyana albishir da cewa na dawo bakin aiki!! ALLAH ya bamu sa'a baki daya.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng