Gwamnatin Jihar Taraba na shirin kirkiro wasu Masarautu a kasar Muri
- Gwamnan Taraba na neman kacaccala masarautar kasar Muri
- Za a ba wasu kananan kabilun da ba su kai ko ina ba Sarakuna
- Wasu na ganin an yi hakan ne domin a rage masu sarauta da iko
Ana tunani Gwamnatin Jihar Taraba ta Mai girma Darius Ishaku ta shirya kirkiro sababbanin masarautu a kasar Muri da wasu bangarori na kasar wanda kuma hakan na iya kawo rikici doriya a kan wanda ake fama da ita a fadin Jihar.
Ana zaman dar-dar a Jihar ta Taraba bayan da bayanai su ka fara fitowa daga Birnin Jalingo cewa Gwamnatin Jihar za ta kacaccala masarautar Muri wanda mafi yawancin mutanen kasar Fulani. Hakan dai ba zai yi wa mutanen dadi ba.
KU KARANTA: Za a gina wani sabon layin jirgin kasa a Najeriya
Kasar Muri ta hada ne da Yankin Lau, Karim-Lamido, Jalingo, Ardo-kola, Zing, Yorro, Ibi, Gassol da karamar hukumar Bari. Yanzu haka Jaridar QuickNewsAfrica ta rahoto cewa ana shirin kirkiro sababbin Masarautu akalla 10 a Kasar.
Hakan dai zai bada dama a gutsura masarautar ta Muri domin a ba sauran kabilun da ke yankin irin su Kona, Jibu, Habe, Lau, Suntai, Kwararrafa, Jibawa, Bunga, Sardaun, Dampar da Kunini kasar kan su. Hakan ya sa wasu su ka fara zanga-zanga.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng