Babu yar makarantan Dapchi da yan Boko Haram suka sace - Kwamishanan Yan sanda
Kwamishanan yan sandan jihar Yobe, AbdulMalik Sumonu, ya bayyana ranan Talata cewa babu wanda aka kashe kuma babu yar makarantan da yan Boko Haram suka sace a harin da suka kai makarantan yan matan garin Dapchi.
Zaku tuna cewa yan Boko Haram sun kai hari makarantar ranan Litinin inda suka kwashe kayan abinci.
Sumonu ya bayyanawa manema labarai a jihar Yobe cewa yan Boko Haram din sun yi garkuwa da maza 3 a karamar hukumar Geidam bayan harin Dapchi.
Ya ce zuwa yanzu, babu labarin bacewan yar makaranta ko daya. “Yar yanzu muna tattara labarai, yawan dalibai da al’umma.”
KU KARANTA: Zaman lafiya ya fara dawowa jihar Benuwe
Rahoto ya nuna cewa jama’an garin Dapchi sun bada tabbacin cewa babu wanda ya rasa ransa duk da cewa yan ta’addan na harbin kan mai uwa da wabi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng