Jam’iyyar PDP ta shiga rudun fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa

Jam’iyyar PDP ta shiga rudun fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa

- Jam’iyyar PDP ta fara lissafin wanda zai tsaya takarar Shugaban kasa

- Akwai kishin-kishin din Obasanjo na so a tsaida Kwankwaso ne takara

- Shi kuma Nyesom Wike ya fi karkata ga wani tsohon Shugaban Majalisa

Mun samu labari cewa yayin da ake fara shiryawa zaben 2019, Jam’iyyar PDP ta shiga rudun fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa inda kan wasu masu ruwa-da-tsaki a Jam’iyyar adawar ya rabu.

Jam’iyyar PDP ta shiga rudun fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa

Gwamna Wike na neman Tambuwal ya dawo Jam’iyyar PDP

Kamar yadda mu ka ji daga Sahara Reporters, tsohon Shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo wanda ko da yake a baki yace ya bar Jam’iyyar, yana neman PDP ta ba mutumin sa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tikitin 2019.

KU KARANTA: 2019: Sanata Marafa yace idan ya ji babu kan-ta zai bar APC

Sai dai Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike wanda shi yake yin yadda ya so a Jam’iyyar a halin yanzu ya fi karkata ne ga Gwamnan Jihar Sokoto watau Aminu Waziri Tambuwal. Ko da dai Tambuwal yace bai da niyyar barin APC.

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo dai ya kafa wata kungiya amma yace ba siyasar 2019 ke gaban ta ba. Shi dai tsohon Gwamnan na Kano kuma Ministan Obasanjo Rabi’u Kwankwaso har yau bai bayyana shirin sa na 2019 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel