Zan tabbatar da managarcin mulki a kowane mataki - Buhari

Zan tabbatar da managarcin mulki a kowane mataki - Buhari

A ranar Talatar da ta gabata ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin tabbatar da sauke alhaki na gudanar da shugabanci a kowane mataki na gwamnati a kasar nan.

Buhari ya yi wannan alkawalin ne a cikin jawaban sa da ya gabatar a taron farko kan yaki da cin hanci da rashawa na jihar Adamawa da aka gudanar a birnin Yola.

Shugaban kasar yake cewa, yana alfahari da gwamnatin sa wajen rashin karaya da tayi dangane da yakar cin hanci da rashawa bisa ga alkawalin da ya daukarwa kasar nan a yayin ratsar da shi bayan nasarar zaben 2015.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari

Buhari yake cewa, "idan ba za manta ba, tun a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015, ya kara jaddadawa 'yan Najeriya cewa, kasar nan cike take da barazana da kuma kalubale musamman ta fuskar cin hanci da rashawa."

KARANTA KUMA: Wasu ma'aurata sun sayar da jaririyar su kan N400, 000 a jihar Abia

"Wanda a yanzu labari ya sha bam-bam daga wancan lokaci zuwa yanzu a sakamakon tashi tsayen da gwamnatin sata yi na daura damarar yakar cin hanci da rashawa."

"Za mu yi ƙoƙarin tabbatar da cewa, mun sauke alhaki na gudanar da shugabanci a dukkan matakan gwamnati a kasar nan."

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wasu ma'aurata sun sayar da jaririyar su kan kudi N400, 000 bayan awannin kadan da haihuwar ta a jihar Imo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel